Dalilan Da Suke Sawa Gwamnati Ba Ta Buga Kudade Domin Ta Raba Wa Jama'a
Da yawan mutane tunani na zuwa cikin zuciyarsu cewa meyasa
gwamnati bazata buga kudade da yawa ba domin ta rabawa jama'a, saboda yanayin a
rage yanayin kunci ? Tunda wadannan kudade dai ba da gwal(gold) ko
lu'u-lu'u(diamond) ake yinsu ba. To a
zahirin gaskiya wannan tunani ne mai kama da abu mai yiwuwa, amma kuma
ba zai yiwu ba. Misali ace a wannan kasar da muke ciki, Masara ne kawai ake
sayarwa, kuma wannan Masaran kana siyanta naira goma(N10) ne. Kuma albashin da
gwamnati ke biyan ko wani ma'aikaci shine naira dari biyar(N500). Kuma kowa da kowa wannan Masaran yake ci
domin rayuwa.
To yanzu mu kaddara cewa bankin kasa(Central Bank) zata buga kudade da yawa domin ta rabawa ma'aikata, albashin kowa ya zama ninki biyu (N1000). A wannan lokaci kanada daman siyan Masara sama da guda daya, kuma haka kowa ma yana da daman siyan wannan Masaran ko guda nawa ne. A wannan lokaci za'a samu tsananin bukatuwar Masara , sannan kuma zata kara tsada. To abun tambaya shine; me yasa baza ayi hayan ma'aikata da yawa ba domin suyi aiki a gonan masara? Eh tabbas za'ayi hakan. To a wannan lokacin albashin ma'aikatan gona zai karu saboda suma suna da bukatan su siya wan nan masaran da firashinta ya karu domin suci. Kenan masaran da kake siya naira goma(N10) a wancan lokacin yanzu firashinta zai karu ya koma naira goma sha biyar(N15). To idan zamu tsaya da kyau mu lura za muga cewa darajar Naira ta fadi kasa warwas, saboda wan nan masaran da kake siya naira goma(N10) a wancan lokacin, itace dai hallau kake siya naira goma shabiyar(N15) yanzu. Zai zamto cewa darajar kudin wannan kasar a fadin duniya ya karye.
| Add caption |
A takaice shine babu wata gwamnati da zata buga kudade da
yawa domin ta fita daga cikin kuncin rayuwa. Ya kamata mu fahimci cewa shi kudi
ba wani abu bane face wani abu mai sauwake alaka a cikin kasuwanci. A maimakon
in baka Doya ka bani Masara, to yanzu kudi ya fitadda darajar kowanne. Saboda
akwai lokacin da zai zamto cewa ni ba Masara nake bukata ba, to kaga yanzu zan
bayar da Doya na sai a bani kudi domin in tafi in sayi abunda nake so.
Da fatan mun karu.
Comments
Post a Comment