Dalilan Da Suke Sawa Gwamnati Ba Ta Buga Kudade Domin Ta Raba Wa Jama'a
Da yawan mutane tunani na zuwa cikin zuciyarsu cewa meyasa gwamnati bazata buga kudade da yawa ba domin ta rabawa jama'a, saboda yanayin a rage yanayin kunci ? Tunda wadannan kudade dai ba da gwal(gold) ko lu'u-lu'u(diamond) ake yinsu ba. To a zahirin gaskiya wannan tunani ne mai kama da abu mai yiwuwa, amma kuma ba zai yiwu ba. Misali ace a wannan kasar da muke ciki, Masara ne kawai ake sayarwa, kuma wannan Masaran kana siyanta naira goma(N10) ne. Kuma albashin da gwamnati ke biyan ko wani ma'aikaci shine naira dari biyar(N500). Kuma kowa da kowa wannan Masaran yake ci domin rayuwa. To yanzu mu kaddara cewa bankin kasa(Central Bank) zata buga kudade da yawa domin ta rabawa ma'aikata, albashin kowa ya zama ninki biyu (N1000). A wannan lokaci kanada daman siyan Masara sama da guda daya, kuma haka kowa ma yana da daman siyan wannan Masaran ko guda nawa ne. A wannan lokaci za'a samu tsananin bukatuwar Masara , sannan kuma zata kara tsada. To abun tambaya sh...